Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai hari akan jirgin kasa tsakanin Armsterdam da Paris


Wata tashar jirgin kasa, a kasar Faransa

Jiya Juma'a wani dan bindiga ya bude wuta akn wani jirgin kasa dake tafiya tsakanin birnin Armsterdan na kasar Holland ko Netherlands zai birnin Paris na kasar Faransa,

Jiya Juma'a wani dan bindiga ya bude wuta akn wani jirgin kasa dake tafiya tsakanin birnin Armsterdan na kasar Holland ko Netherlands zai birnin Paris na kasar Faransa, ya raunana mutane uku kafin fasinjoji suka fi karfinsa ciki harda wasu sojojin Amirka guda biyu.


Jami'an kasar Faransa sunce ba'a san dalilin daya sa dan bindigan ya dauki wannan mataki ba, amma sunce yan sandan dakile aiyukan ta'adanci suna jagoranci binciken da ake yi.


Ministan harkokin cikin gidan Faransan yace an kama dan bindigan ne a wata tashar jirgin kasa a birnin Arras. Yan sanda sunce mutumin shekaransa ashirin da biyar da haihuwa, kuma shi dan asalin kasar Morocco ne, kuma yana dauke da bindiga mai sarrafa kanta da kuma wuka.

XS
SM
MD
LG