Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Sudan


Wata motar sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan.

Hadin gwiwar kwamatin lura da ayyukan kare zaman lafiya na tarayyar Afirka da MDD a yankin Darfur kasar Sudan ya bada rahoton cewa wasu ‘yan bindigar da ba’a tantance dasu ba sun kaiwa sojin kiyaye zaman lafiya hari jiya Talata.

Hadin gwiwar kwamatin lura da ayyukan kare zaman lafiya na tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur kasar Sudan ya bada rahoton cewa wasu ‘yan bindigar da ba’a tantance dasu ba sun kaiwa sojin kiyaye zaman lafiya hari jiya Talata.

Sun kuma jikkata guda daga cikin sojin kiyaye zaman lafiya ya sami rauni mai tsanani.

Hadin gwiwar kwamatin na Tarayyar Afirka da MDD ya bada sanrwar kai harin ne bayan da ya aike da sakon gaggawa ga Gwamnatin Sudan da ta gaggauta binciko wadanda suka kai wannan hari domin gurfanar dasu gaban shari’a.

Jakadan MDD na musamman Ibrahim Gambari ya nuna takaicin kai wannan hari a Darfur a dai dai lokacin da ake kokarin maido dazaman lafiya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG