Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 14 Sun Mutu A Harin Kunar-Bakin-Wake Yau Laraba A Maiduguri


Ma'aikatan agaji na jiran zuwan gawarwaki wadanda harin Bom din da aka kai a Maiduguri ya hallaka 16, ga Oktoba 2015.

Mutane akalla 14 sun mutu yau laraba a lokacin wasu hare-haren kunar-bakin-wake a garin Maiduguri dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wata majiyar 'yan sanda ta ce mutane 14 ne suka mutu a wannan lamarin tare da jikata wasu 65 da yanzu suke asibitoci daban daban.

Shaidu dake wurin sun ce mutane hudu ne suka kai hari kuma akwai akalla mace daya cikin maharan.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta fada cikin wata sanarwar da jami'in yada labaranta na yankin arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim, ya bayar cewa mutane 65 sun ji rauni a wannan lamarin da ya faru da misalin karfe 5 da minti 5 na yammacin yau.

Babu watanda ya dauki alhakin kai wannan harin, amma kuma bangaren Abubakar Shekau na kungiyar Boko Haram ta sha daukar alhakin kai hare-haren kunar-bakin-wake a wannan unguwa ta Muna dake Maiduguri.

Da zara mun samu karin bayani zamu sanar da ku

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG