Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Wa Mataimakin Shugaban Afghanistan Hari


Amrullah Saleh

Wani hari da aka kai wa mataimakin shugaban Afghanistan, Amrullah Saleh, a Kabul da safiyar Laraba 9 ga watan Satumba, ya yi sanadiyyar kisan akalla mutane 10 tare da raunata wasu da dama

Wadanda suka raunata dai galibin masu tafiya a kafa ne a daidai lokacin da aka fi yawan samun zirga zirgar jama’a da safe, a cewar jami’ai daga ma’aikatar cikin gidan Afghanistan.

Jami’ai sun ce fashewar da ta auna jerin gwanon motocin Saleh wani bom da aka binne a bakin hanya ne ya yi sanadinta.

Saleh ya tsira daga harin a cikin motarsa mai kariyar harsashi amma ya samu ‘yan raunuka a fuska da hannayen sa.

Inda aka kai masa harin
Inda aka kai masa harin

Ba da daɗewa ba bayan harin, Saleh ya sanya wani saƙon bidiyo akan shafin Facebook inda ya bayyana abinda ya faru.

"Fashewar ta yi karfi sosai har ta narkar da tagogin motata," a cewar Saleh. Ya kara da cewa yanzu ya fahimci yadda jami'an tsaron kasar ke fuskantar irin wannan yanayin a kullum.

Ya kuma jajanta wa mutanen da suka rasa rayukansu ko dukiyoyinsu sakamakon harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG