Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Wani Farmaki Mai Kama da Juyin Mulki a Kasar Gambiya

Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya
Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya

Mazauna Banjul, da kuma jami’an difilomasiya a babban birnin na Gambiya, sun bayar da rahotan barin wuta mai yawa a unguwar da fadar shugaban kasar take cikin wannan birni.

Wasu shaidun sunce suna kyautata tsammanin akwai hannun dakaru masu tsaron shugaba Yahya Jammeh a harbe harben da ya ‘barke a safiyar yau Talata a birnin Banjul.

Har yanzu dai babu wani tabbacin cewar wannan yunkurin juyin mulki ne, kuma an samu rahotannin dake sabawa juna a kan ko an kawo karshen wannan fadan.

Wani rahoto na cewa shugaban kasar Yahya Jammeh baya kasar alokacin da harbe-harben ke faruwa, ana tsammanin yana kasar Faransa ko Dubai.

Kasar Gambiya dai karamar kasace data samu ‘yancin kanta daga mulkin mallakan Ingila, tana makwabtaka da kasar Sanigal.

Shugaban kasar ya karbi mulki ne a shekara ta alif dari tara da casa’in da hudu a juyin mulki, wanda yake fuskantar suka kan batutuwa na keta hakkin bil adama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG