WASHINGTON, DC —
A yayi da ‘yan takarar neman mukaman siyasa, ke zafafa fafutukar yakin zabe, a daya gefen ‘yan ta’adda suma sun kaddamarda kai hare-hare kan ‘yan siyasa.
Hari na baya-bayan nan shine wanda wasu bata gari suka kai gidan dan takarar neman kujerar Gwamnan jihar Gombe, a inuwar jamiyyar APC, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya.
Shima Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, a kwanakin baya wasu sun kai masa hari sailin da ya ziyarci garin Kashere .
Biyo bayan wannan hare-hare rundunar ‘yan sandan jihar ta Gombe, ta bukaci ’yan siyasa dasu iya bakinsu wajen amfani da kalamai domin gujewa tashi hankali, ta kuma ce zata tabatar da tsaro a jihar ta kuma yi furucin hukumta duk wanda aka kama da neman tada fitina.