Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kalubalanci Koroma Game Da Korar Mataimakinsa


Ernest Bai Koroma, Shugaban kasar Saliyo

Bayan korar mataimakinsa, shugaban kasar Saliyo, Ernest Boi Koroma na fuskantar suka daga 'yan majalisun kasar.

‘Yan majalisun da suka fito daga bangaren jam’iyyar adawa a kasar Saliyo sun kalubalanci shugaban kasar Ernest Boi Koroma game da korar mataimakinsa Sam-Sumana da ya yi, inda suka ce wannan yiwa dokar kasar karan-tsaye ne.

Babban sakataren ‘yan jam’iyyar adawar kasar Sulaiman Banja-Sie ya fadawa Muryar Amurka cewa sun fara kalubalantar wannan hukunci na a gaban babbar kotun kasar.

Sannan kuma suna kira ga ‘yan majalisar kasar da su fito zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da wannan al’amari yana mai cewa bakaken hulunan da za su saka a kawunansu alama ce ta nuna rashin amincewarsu.

Ya jaddada cewa jam’iyyarsu mai bin doka da oda ce don haka ba fito na fito za su yi da kowa ba.

Sun ce sun bawa gwamnatin kwanaki bakwai kacal su janye maganar korar Sam-Sumana wanda kuma jam’iyyarsa ta kora bisa zargin su ga don ta da zaune-tsaye da kafa sabuwar jam’iyya.

‘Yan adawar sun ce shugaban kasar ya yi amfani da dokar kundin tsarin mulkin da ba a amfani da ita wajen tsige Sumana.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG