Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dinbin Jiragen Ruwa Masu Satar Man Najeriya


Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

A cigaba da kokarin kawo karshen yawan sace man Najeriya da wasu gaggan barayi ke yi ta wajen amfani da wasu dabarun zamani, Rundunar Sojin Ruwa ta Kasar, da hadin gwiwar Hukumar Kamfanin man kasar (NNPC), ta fara yin nasara.

Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, ta sanar cewa ta Kama wasu jiragen ruwa goma sha biyu, da ke dakon mai da aka sato a yankin Neja Dalta, a wani samamen hadin gwiwa da ta kaddamar a yankin mai suna Operation Dakatar da Barawo.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya, Commodore Ayo Adedatun, ya ce rundunar ta kaddamar da wannan aiki na musamman na yakar masu satar danyen mai a yakin na Neja Delta ne da hadin gwiwar babban Kamfanin Man Najeriya, NNPC. An kaddamar da shirin ne a watan Afirilu na wannan shekarar, kuma an samu gagarumar nasara wajen kama barayin mai da kuma wasu jiragen ruwa tara na dakon man da aka sato.

Ya a kuma kama wasu barayi a Fatakwal da Yanagua na jahar Bayelsa da Worri. An kuma kama wani man da aka sato daga yankin tsibirin Bonny na jahar Rivers. Rundunar ta ce matasan yankin na dada zama babbar matsala gare ta. Y ace daya daga cikin kalubalen da su ke fuskanta shi ne rashin samun hadin kai daga matasa, da kungiyoyin sa kai da kuma sauran al’ummomin yankin.

Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sakkwato:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG