Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Jagoran 'Yan Adawar Rasha


Jagoran 'yan adawar Rasha Alexei Navalny

Dambarwar siyasar kasar Rasha ta dau wani sabon salo bayan kama fitaccen jagoran 'yan adawa kuma matashi mai matukar farin jini Alexei Navalny. Navalny ya shirya zanga-zangar yin watsi da zaben kasar da ake shirin gudanarwar a watan gobe.

‘Yan sanda a birnin Moscow sun damke jagoran ‘yan adawa Alexei Navalny, a wani gangamin da ya shirya na nuna rashin amincewa da zaben shugaban kasar Rasha da za a gudanar a watan Maris.

Navalny ya aika da wani sako ta kafar twitter mai cewa, “An kama ni,” sannan ya yi kira ga magoya bayansa su shiga zanga-zangar.

Tun da farko a yau dinnan Lahadi ‘yan sanda su ka kutsa cikin hedikatar kwamitin yakin neman zaben Navalny, inda wani faifan bidiyon da aka yada kai tsaye ya yi ta nuna yadda ‘yan sanda su ka yi ta tambayoyi ma ma’aikata tare kuma da kama wasunsu.

Jagoran ‘yan adawar ya ce a kaurace ma zaben na watan Maris, wanda ya bayyana da shirme.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG