Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane A jihar Adamawa


Jami’an tsaron jihar Adamawa sun kama mutum 26, wanda uku daga cikin su kwararru ne wajen kashe mutane, tare da wani matashi mai kimanin shekaru 15, wanda ke kwarmatawa da kuma bada bayanai ga masu garkuwa da mutane, ana biyansa naira dubu hamsin akan kowane mutum da suka sace.

Sauran wadanda aka kaman sun hada da wadanda ake zargi da sace - sacen motoci a ciki da wajen jihar.

Wani babban jami'in hukumar 'yan sanda DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce, yanzu haka rundunan hadin gwiwar da aka kafa sun soma shiga mabuyar masu garkuwa da mutane da kuma sauran bata gari.

Haka zalika Rundunan tsaron farin kaya ta “Civil Defense” ta kama wasu ‘yan fashi da makami ciki harda wadanda suke 'yan uwan juna.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG