Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Masu Farautar Barewa A Nijar


Barewa

Hukumar gandun daji ta jihar Damagaram a jamhuriyar Nijar ta cafke wasu mautane dauke barewa kimanin guda takwas a cikin mota, wasu kuma a akan babur a yankin Tanut.

Dokar kasar Nijar ta hana farautar Barewa sai in da kwakkwaran dalili. Mutanen dake farautar irin wadannan dabbobin suna sayar da su ne ga masu hannu da shuni,

Kanal Abdulrahaman Yakuba, jami’in gandun daji a jihar Damagaram, yace sun kama motar fari da barewa guda hudu a ciki amma biyu daga cikinsu sun mutu daga baya kuma suka cafke wasu guda shida a lokuta dabam dabam. Jami’in ya kara da cewa yanzu haka mutane biyu da aka kama da dabbobin na hannu kuma ana shirin mika su gaban hukuma.

To ko menene makomar wadannan dabbobin da aka kama? Kanal Abdulrahaman yace za a maida su daji don su ci gaba da rayuwa da sauran ‘yan uwansu.

Ya kara da yin kira ga jama’a akan su taimaka wajen sanar da hukuma akan duk wani abu da suka gani da zai iya cutar da wadannan dabobin.

Musa Mudi, wakilin wata kungiya da ake kira kwalliya, mai yaki da farauta a Nijar yace zasu bada goyon baya wajen ganin an kare wadannan dabbobin, saidai yace babbar matsalar da suke fuskanta ita ce yawancin lokuta basa samun bayanai akan lokaci. Ga Karin bayani a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG