Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Sojojin Burkina Faso 10 Dake Alaka Da Kai Wani Hari


Sojojin Burkana Faso

Wani jami'in soja a Burkina Faso ya ce an kama sojoji 10 dangane da wani samamen da aka kai da asubahin ranar Jumma'a, wajen wani wurin ajiye makamai, wanda ke wajen birnin Ouagadougou.

Wannan samamen da aka kai wurin adana makamai da ke Yimbdi, ya zo ne mako guda bayan da wata kungiyar ta'addanci mai alaka da al-Ka'ida ta kashe mutane akalla 29 tare da raunata wasu da dama, ciki har da wasu 'yan kasashen waje da dama, a wani babban otal da kuma wani wurin shan shayi da ke kusa.

Mai magana da yawun sojin, Willy Youmeogo ya fadi jiya Asabar cewa dukkan mutane 10 da ake zargin su na da hannu a samamen da aka kai wurin adanar makaman, tsoffin dogarawan tsaron fadar Shugaban Kasa ne. Ya ce an kuma kama wani shugaban addini.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG