Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu 'Yan Boko Haram A Legas


'Yan Kungiyar Boko Haram Da Ake Nema Ruwa A Jallo

Mai Kanuri na Ijora dake jihar Legas ya shaidawa Muryar Amurka yadda suka cafke wasu 'yan kungiyar Boko Haram da sunayensu ke cikin jerin sunayen 'yan kungiyar su dari da ake nema tamkar ruwa a jallo.

A firar da ya yi da manema labarai Mai Kanuri na Ijora Alhaji Mustapha Muhammad ya bayyana sunayen wadanda aka kama.

Mutanen sun hada da Ibrahim Ali, Abubakar Ahmed, Gogwai Kansilo, Ibrahim Muhammad, Bana Gana, Bulama Ali da Adam. Ranar Juma'ar da ta gabata aka kamasu.

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,

An dai kama mutanen ne a wurare daban daban, a wuraren da suke samun mafaka musamman wuraren da ake samun 'yan arewacin Najeriya.

Adam daya daga cikin wadanda aka kama kuma shugabansu an kamashi ne a harabar wani Coci a boye a cikin wata kwantena.

Mai Kanuri yace suna da hakimai a kowane bangare a Legas. Da zara wani daga kauyensu ya isa Legas sai ya je wurin da hakiminsa yake idan kuma an gane dan Boko Haram ne sai a kamashi a kaiwa Mai Kanurin.

Mai Kanuri yace suna aikin ne da hadin gwuiwar jami'an tsaro kamar yadda wani dan asalin jihar Borno ya tabbatar. Malamin da baya son a fadi sunansa ya ce da gaske ne ana kama 'yan Boko Haram a Legas. Yace ko satin da ya wuce an kama kusan goma.

Tuni aka tasa keyar wadanda aka kama zuwa jihar Borno ga hannun rundunar tsaro dake yaki da kungiyar Boko Haram

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG