Da misalin karfe 3:30 agogon Najeriya, aka gudanar da sallar jana'izar marigayi tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, wanda ya rasu jiya a asibitin kasa da ke birnin tarayya, Abuja.
Bayan an kai gawar tasa gidanshi da ge garin Shagari a karamar hukumar Shagari ta jahar Sakkwaro, 'yan uwa da abokan arziki sun halarci jana'izarsa. Mahalarta jana'izar sun hada da Gwamnonin jahohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, kana da tsohon gwamnan jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
An yi mishi farentin ban girma kamun aka bisne gawar tasa a wani bangare da aka ware na musamman a cikin gidanshi da ke garin na Shagari.
Ga tattaunawar wakilin sashen Hausa na muryar Amurka a jahar Sakkwato Murtala Faruk Sanyyina da Yusuf Aliyu Harande jim kadan bayan kammala sallar jana'izar.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.