Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Gasar Masana Kimiya Da Fasaha Na Afirka A Kigali, Rwanda


Dr Conrad Tankou daga hagu wanda ya lashe gasar
Dr Conrad Tankou daga hagu wanda ya lashe gasar

A taron gasar masana kimiya da fasaha na nahiyar Afirka da aka yi a Kigali kasar Rwanda da ya samu halartar mutane 1600, Dr. Conrad Tankou na kasar Kamaru ya zo na daya inda ya samu kyautar dalar Amurka dubu 25

Makon jiya ne aka kammala taron gasar masana kimiyya da fasaha na kasa da kasa, da galibin mahalarta sun fito ne daga nahiyar Afirka. Mutane fiyeda 1,600 ne suka hallara a Kigali babban birnin kasar Rwanda.

Taron wanda shine karo na biyu, mai lakabin fitaccen misanin kimiyya da fasaha na gaba daga Afirka, ko "the next Einsten, da turanci, cibiyar lissafi da kimiyya ta Afirka ta kirkiro shi, da zummar karfafa gwuiwar masana kimiyya su bullo da kere-kere-a fannoni daban daban ganin acewar cibiyar, an bar nahiyar Afirka a baya.

Wani Likita dan kasar Kamaru daga yankin Baminda mai suna Conrad Tankou ne, ya lashe kyauta mafi soka ta fuskar kiwon lafiya, ta dalar Amurka dubu 25, saboda ya kera wata na'ura da zata gano cutar daji dake addabar mata kusan dubu 7 a duk shekara, itace cuta ta biyu da take addabar mata a Kamaru, tana kuma illa ne ga sassa dake kusa da mahaifa.

Dr. Tankou ya ce bai zaci zai kai wannan mataki ba, saboda irin kalubale da ya fuskanta. Conrad ya ce 'yanuwansa likitoci sunki su bashi hadin kai.

Baya ga haka, Likitan yace, akwai wata damuwa ta daban daga 'yan nahiyar wadanda basa ganin 'yan nahiyar zasu iya samar da wani abu da zai samar waraka. Komi a ganin su sai idan ya fito daga turai.

Cikin kalubalen amfani da na'urar sun hada harda rashin internet akai-akai, kuma kashi 25 cikin dari na 'yan Kamaru ne suke da internet.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG