Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Farashin Man Fetur a Najeriya


Kamfanin kasuwancin albarkatun Man fetur na Najeriya PPMC, ya fito da wata sanarwa da ke nuni da karin farashin dakon Man fetur daga depot zuwa Naira 151.56 akan kowace lita. sabanin Naira 138.62 da ake dauka a baya.

Sanarwar karin kudin dakon Man fetur din wadda aka rabawa manema labarai na dauke da sa hannun Manaja mai kula da depot mai suna D.O Abalaka. Kuma kamfanin PPMC dake zaman wani reshe na ma'aikatar Man fetur ta kasa NNPC, wacce ita ma ta amince da karin.

Shugaban Kungiyar Man fetur masu zaman kansu ta IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingaru, ya ce samun takardar sanarwar ke da wuya, suka yi wa ‘yan kungiyar su umurni da cewa daga yanzu su sayar da Man fetur akan Naira 158 zuwa Naira 160 a kan kowacce lita daya.

Mai nazarin al'amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, ya ce gwamnati ta fito kiri kiri ta nuna rashin tausayi ga talakawa wadanda sune suka zabe ta. Ya kara da cewa a cikin yan watanni an yi kari har sau uku, ga annobar coronavirus ga hauhawar kudaden kayan masarufi, to da wanne talaka zai ji?

Amma ga tsohon mukaddashin shugaban Ma'akatan Man fetur ta Kasa Kwamarad Isa Tijjani, ya ce ba a karin kudin mai mafita ta ke ba, abin da ya kamata gwamnati ta yi shine tayar da matatun Man kasar idan ana so a samu sauki.

Wasu masu sayar da Man fetur a kasuwar bayan fagge sun baiyana cewa kafin a kai ga yin wannan karin, suna sayar da Man fetur lita goma a kan kudi Naira 1,800.

Sanarwar ta ce daga ranar biyu ga wannan wata na Satumba karin ya fara aiki, kuma an kaiyade kudin ne a bisa karfin farashin Mai a kasuwar duniya.

Domin Karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG