Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Kama Wasu Mutane Biyu Sakamakon Harin Da Aka Kai A London


An Kunna Kyandir Akan Gadar Westminster Bridge Kwana Daya Bayan Hari A London.

Yau Juma’a Jami’an ‘Yan Sanda a London sunce sun kama karin wasu mutane guda biyu dangane da harin da aka kai a kusa da Majalisa.

Kwamandan Jami’an ‘Yansandan Hana Afkuwar Aiyukan ta’addanci Mark Rowley ya bayyana kamen a matsayin mai muhimmanci, koda yake bai bada wani cikakken bayani ba . Yace mutane 9 na nan a tsare kuma an saki wani mutum guda.

Jami’an ‘Yan sanda sun bayyana wanda yakai harin ya kuma kashe mutane hudu a kusa da Majalisa da sunan Khalid Masood, dan kasar Birtaniya wanda ya shiga cikin addinin Islama kuma yana da tsohon tarihin aikata manyan laifuffuka na mallakar makamai da sauransu.

Rowley yace sunan Masood na yanka shine Adrian Russell Ajao. Kungiyar Da’esh tace Masood, dan shekara 52 Sojanta ne wanda ya amsa kiran kai hari kan fararen hula da kuma jami’an soji a kasashen da suke kawance da Amurka masu yakar Kungiyar ta Da’esh.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG