Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kasa Warware Rikicin APC A Maajalisar Wakilai


Kakakin Majalisar Wakilai Dogara Yakubu.

Barakar da aka samu tsakanin ‘ya’yan Jamiyyar APC kan batun zaben shugabanni a Majalisar Wakilai na kara Kamari. A taron manema labarai da suka kira a Abuja jiya Lahadi, ‘yan goyon banyan Kakakin Majlisar Yakubu Dogara da suke kiran Kansu sun ce an yi sulhu, sai dai nan da nan masu goyon bayan FemiI Gbajabiamila da su kuma suka ke kiran kansu suka ce ba haka zancen yake ba.

Mai Magana da yawun bangaren “Equity Group”, Abdulmumuni Jibril ya bayyana yadda aka yi rabon mukaman inda aka ba Ado Doguwa APC Kano jagoran majalisa, Buba Jibrin APC Kogi mataimakin jagoran majalisa, Palli Ireasia APC Edo South -South, gagarabadau da kuma Chika Okaffor APC Imo mataimakin gagarabadau.

Bayan wannan sanarwar ne masu goyon bayan Femi Gbajabiamila suka kira taron manema labarai inda suka ce, wannan batun bai taso ba. Kakakin kungiyar Ahmed Baba Kaita yace zasu koma majalisa ranar Talata, kuma suna sa ran, idan aka bi tsarin majalisa da abinda duka ta tanada, za a bada dama ga ‘ya’yan jam’iyar APC suje su yi zabe, duka wanda Allah ya ba muddar an bi wadannan ka’idojin za a sami masalaha.

Ahmed Baba Kaita yace, fargaban da jama’a suke yi shine kada abinda ya faru a majalisar dattijai ya sake faruwa a majalisar wakilai, inda shugaban majalisar dattijai Saraki ya zauna ya kira sunayen mutane yace sune shugabannin majalisar ba tare da la’akari da abinda kundin tsarin mulkin kasa ko kuma dokokin tsarin gudanar da ayyukan majalisa suka ce ba.

Yace sun jajirce cewa, tilas ne a dauki wannan matakin wajen zaben shugabannin majalisar , bisa ga cewarshi, Magana ce ta kura cikin gwado, ba batun wanene zai rike mukami bane.

Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Madina Dauda ta hada mana.

Rikicin Majalisar Wakilai-3:36"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG