Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Abubakar Shekau Tun Bara - inji SSS


Wanda yake ikirarin shi ne Abubakar Shekau shugaban Boko Haram

Biyo bayan bidiyo da Boko Haram ta fitar akan daliban da ta sace Marylin Ogah mai magana da yawun 'yan sandan leken asiri ko SSS tace shugaban kungiyar Boko Haram na yanzu ba Abubakar Shekau ba ne.

Bayan da kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyo akan daliban da ta sace hukumar SSS tace wanda yake ikirarin shi ne Abubakar Shekau karya yake yi.

Mai magana da yawun hukumar SSS Marylin Ogah a karon farko ta karyata wanda ya ke kiran kansa Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram.

Marylin Ogah tace tun bara aka kashe Abubakar Shekau da Abubakar Kaka a wani gumurzu da suka kara da jami'an tsaron Najeriya. Tace yanzu kungiyar ta zama kamar ta 'yan kasuwa. Kowa ma na iya kiran kansa dan Boko Haram har ma ita idan ta ga dama. Tace bayan an kashe Abubakar Shekau wanda ya zama shugaban kungiyar shi ya dauki sunan yana anfani da shi.

Marylin Ogah ta cigaba da cewa kungiyar tamkar kasuwanci ta keyi da sata da fashi da makami inda take wawure dukiyoyin jama'a da sunan addini. A zahirin gaskiya bata addini ba ce ta 'yan gungun 'yan ta'ada da barayi ne.

Ta kara da cewa "mun sansu kuma su ma sun sanmu. Idan lokaci yayi zamu yi cikakken bayani".
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG