Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Fashe Fashe A Mogadishu Sun Halaka Akalla Mutane 11.


Wani sojan Somaliya yake gittawa inda aka kai harin na yau Asabar 28 ga wtaan Oktoba.

Al-shabab ta tada nakiyoyi a kofar wani fitaccen O'tel da ake kira Nasa Hablod, kamin su kutsa ciki.

A Somaliya, akalla mutane 10 ne suka halaka ciki harda jami'an gwamnati, lokacinda wasu motoci biyu da aka dankarawa nakiyoyi suka yi binidga a babban birnin Mogadishu a yau Asabar, makonni bayan wani mummunar hari da aka kai a birnin wanda ya halaka fiyeda mutane 350.

Fashewar farko ta auku ne a fitaccen O'tel din da ake kira Nasa Hablod, wadda mayakan al-shabab dauke da bindigogi suka kutsa ciki bayan da suka tada nakiyoyi da suka dankarawa wata mota a kofar shiga O'tel din.

Jami'an kasar suka ce akalla 'yan binidga uku suna cikin O'tel din suna ci gaba da musayar wuta da jami'an tsaro.

Ayan Abdi Ahmed, wacce take cikin O'tel din lokacinda aka kai harin, tace taga maharan sun yi shigan jami'an gwamnati suka shiga O'tel din inda minisotci da manyan jami'an gwamnati suke, suna kashe mutane daya bayan daya.

Tace ta buya, ta sami dan sarari ta gudu daga O'tel din. Ta yiwa Allah godiya ta tsira amma tace akwai mutane cikin O'tel din da kuma a waje wadanda suka halaka. Ayan tace ta ga gawarwaki akalla 11.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG