Accessibility links

An kashe akalla mutane goma a kasar Kenya

  • Jummai Ali

Gawarwarkin wasu da aka kashe a lokacinda aka hare hare akan majami'u a Kasar Kenya Lahadin nan

Jami’ai a arewa maso gabashin Kenya sunce an kashe akalla mutane goma a lokacinda wasu mahara suka jefa gurnati akan wasu majami’u guda biyu.

Jami’ai a arewa maso gabashin Kenya sunce an kashe akalla mutane goma a lokacinda wasu mahara suka jefa gurnati akan wasu majami’u guda biyu.

Hukumomi sunce mutane arba’in ne suka ji rauni a harin da aka kai yau Lahadi akan cocin darikar Roman Katolika da kuma cocin African Inkand a Garissa kusa da kan iyakar kasar da Somaliya.

Tun dai watan Oktoba, lokacinda jami’an tsaron Kenya suka tsalaka suka shiga Somaliya domin taimakon kasar fafatwa da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab, kasar Kenya din keta fama da matsalar har hare hare da bama bamai da sassace mutane.

XS
SM
MD
LG