Accessibility links

An kashe Limamin nan mai tsattsauran ra'ayi, haifaffen Amurka, a Yemen

  • Ibrahim Garba

Marigayi Anwar al Awlaki

Wani ba-Ameriken Malamin addinin Musuluci mai tsattsauran ra’ayi

Wani ba-Ameriken Malamin addinin Musuluci mai tsattsauran ra’ayi, da gwamnatocin Yemen da Amurka ke nemarsa, ya mutu a wani harin da ake ganin jirgin saman Amurka da ba matuki ciki ne ya kai.

Ma’akatar Tsaron Yemen t ace an hallaka Anwar al-Awlaki mai alaka da al-Kaida da wasu da dama da ake kyautata zaton mayakan sa kai ne. Ba a bayar da cikakken bayanin yadda aka kai harin da kuma inda aka kai ba zuwan lokacin hada labarin.

Gwamnatin bata bayar da karin haske game da mutuwar ba, wadda wani jami’in gwamnatin Amurka da aka sakaya sunansa ya tabbatar.

Majiyoyi daga wasu kabilu da kuma kafafen jami’an tsaron kasar Yemen sun ce an kashe Awlaki ne da safiyar yau Jumma’a a wani harin jirgin saman da aka auna kan wata tawagar ‘yan al-Qaida a gabashin kasar.

Rahotanni sun ce wani jirgin Amurka ne ya kai harin. A baya ma Amurka ta sha kai hare-haren jiragen da ma matuki ciki da takan auna kan ‘yan al-Qaida a kasar.

Da Amurka da Yemen sun yi ta neman Awlaki saboda zarginsa da hannu a hare-haren ta’addanci, ciki hard a wani yinkuri na tarwatsa wani jirgin Amurka a 2009.

XS
SM
MD
LG