Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 17 a wajen walimar aure a Afghanistan


Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan daga hannun dama

shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan yayi Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kai wajen walimar aure da sanyin safiyar yau Asabar a wani lardi dake arewacin kasar daya kashe mutane goma sha bakwai.

Da kakkausan harshe, shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan yayi Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kai wajen walimar aure da sanyin safiyar yau Asabar a wani lardi dake arewacin kasar daya kashe mutane goma sha bakwai.

A wata sanarwar daya gabatar, shugaba Karzai yace cikin wadanda aka kashe a yau asabar a lardin Samangan, harda Ahmad Khan Samangani wani dan Majalisar wakilai da Janaral Mohammed Khan, direktan hukumar leken asirin lardin Samangan. Haka kuma daga cikin wadanda suka ji rauni harda wani wakilin Majalisar wakilai da wani kwamandan yan sanda da wani tsohon gwamna.

Shugaba Karzai ya kafa wani kwamiti da zai binciki wannan harin ta’adanci. Ana waliman auren ne a Aybak baban birnin lardin aka kai wannan hari. Hukumomi sunce mai harin kunar bakin waken ya shiga inda ake waliman, ya rungumi Samangani kafin ya tarwatsa kansa.

Haka kuma a yau asabar an kashe wani sojan kungiyar kawancen tsaro ta NATO a sakamakon wani hari da yan tawaye suka kai a gabashin Afghanistan.

XS
SM
MD
LG