Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 3 da raunana 41 Lahadin nan


Irin barnar da hare haren yan kungiyar Boko Haram ke yi a Nigeria ke nan

Kungiyar Boko Haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hari akan coci coci guda biyu Lahadin nan, harma aka kashe mutane uku da raunana mutane arba'in da daya.

Kungiyar yan yakin sa kai ta Boko Haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hare hare akan majami'u guda biyu a ranar Lahadi, harma aka kashe mutane uku da raunana mutane arba'in da daya.

A wajen wani taron wayan tarho sa'o'i bayan an kai hare haren, wani mai magana da yawun kungiyar Boko Haram ya fadawa yan jarida cewa kungiyarsa ce keda alhakin kai hare haren.

Daya harin akai ne a birnin Jos inda wani mai harin kunar bakin wake ya tada bam din da aka boye cikin wata mota a harabar wata majami'a

Daya harin kuma a garin Biu jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria aka kai. A can shedun gani da ido sunce wasu 'yan bindiga ne suka bude wuta akan masu ibada, shima a wata majami'a harma aka kashe akalla mutum guda.

XS
SM
MD
LG