Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 6 Akan Iyakar Kamaru Da Najeriya


Nigeria Cameroon Raids

Mutane 6 ne aka kashe akan iyakar Najeriya da Kamaru a lokacin da 'yan awaren masu magana da harshen ingilishi suka yi kokarin kai wa jami'an tsaron kasar ta Kamaru hari.

Wannan hari ya faru ne lokacin da aka kai wa wani shingen sojan da ke garin na Mamfe hari a kasar ta Kamaru.

An kai harin ne bayan da wata tawagar Najeriya ta musamman ta tabbatar wa kasar ta Kamaru cewa za su hada hannu domin yaki da ta'addanci a wannan wuri.

Dama kasar ta Kamaru ta jima tana kokawa akan yadda ‘yan awaren suke amfani da bakin iyakar Najeriya a masayin wurin yin atisayensu.

Wakilin wannan gidan radiyon mai aiko da rahotanni daga kasar ta Kamaru, Moki Edwin Kindzeka, ya ce Ministan sadarwa kuma mai Magana da yawun gwamnati Issa Tshiroma ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya kuma ce dubban matasa ne dauke da makamai da suka hada da bindigogi da adduna, da kwari da baka suka kai wa’yan sandan dake yankin na Mamfe hari

Harin ya auku ne a daren ranar Alhamis din da ta gabata.

Tchiroma ya ce sakamakon haka ne dan sanda guda ya mutu kana 5 daga cikin maharan suma sun mutu, sannan wasu da dama musammam daga cikin maharan suka samu raunuka.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG