Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Biyu A Jami'ar California Ta Amurka


UCLA inda aka kashe mutane biyu

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wani harbin bindiga da ya auku a dakin kwaji na masu koyon ilimin injiniya a Jami'ar California ko UCLA a takaice dake birnin Los Angeles

Jiya Laraba ne aka harbe mutane biyu cikin jami'ar ta California lamarin da ya sa 'yansanda suka rufeta na wani dan karamin lokaci.

Babban fifeton 'yansandan birnin Los Angeles Chief Charlie Beck yace wanda ya harbe wani mutum shi ya juya ya harbe kansa. Yace duka wadanda suka mutun maza ne.

Wani jami'in tsaro ya shaidawa jaridar The Los Angeles Times cewa bisa ga gawarwakin da ya gani shehun malami ne dalibinsa ya harbeshi kafin shi dalibin ya kashe kansa.

Lamarin ya auku ne a wani karamin ofis dake cikin ginin sashen koyan aikin injiniya. Babban sifeton 'yansanda yace an samu bindiga daya tare da wata wasika da aka rubuta. Kawo yanzu 'yansanda basu tantace mutanen ba.

Ita dai jami'ar ta UCLA tana yankin Los Angeles da ake kira Westwood ne. Tana da dalibai kimanin 40,000. Wannan harin ya auku ne mako daya kafin dalibai su fara jarabawar karshen shekarar karatu kana su tafi hutu.

UCLA
UCLA

XS
SM
MD
LG