Accessibility links

An harbe mutum 12 a jihar Colorado nan Amirka

  • Jummai Ali

Inda aka yi harbin fada kan mai uwa da wabi a wani gidan sinima a Aurora, jihar Colorado nan Amirka

'Yan sanda a jihar Colorado nan Amirka, sunce mutane goma sha biyu aka harbe har lahira, akalla talati da takwas kuma suka ji rauni, a harbe harben da aka yi a wani gidan sinima a garin Aurora kusa da birnin Denver

'Yan sanda a jihar Colorado nan Amirka sunce an harbe mutane goma sha biyu da raunana akalla mutum talatin da takwas a harbin fada kan mai uwa da wabi da wani matashi ya aikata a wani gidan sinima, a garin Aurora kusa da birnin Denver,

Hukumomin sunce an fara nuna fim mai suna " The Dark Knight Rises" juma'a nan, ke nan a wani gidan sinima a Aurora, wani mutum daya rufe fuskarsa a gaban siniman dake dankare da mutane, ya jefa gongonin barkonon tsohuwa, sa'anan sai ya fara harbin fada kan mai uwa da wabi. Shedun gani da ido sunce harma ya kashe wani jariri.

Daga bisani, yan sanda suka kama maharin a wajen ajiya motoci a harabar gidan sinaman. Sunce shi wannan maharin, wanda matashi ne, yana rike da bindiga samfurin rifle da kuma wani karamin bindiga. Shugaban yan sanda Aurora Daniel Oates ya fadawa wani taron yan jaridar cewa mutum daya ne ya aikata wannan danyen aikin, sabanin rahotanin farko da aka yayata cewa, kila akwai wani wanda ya taimaka masa.

Shugaban yan sanda, yace shi wannan mutumin da ake zargi, ya fadawa masu bincike cewa yana da nakiyoyi a gidansa. Sa'o'i bayan anyi harbe harben ne gidajen talibijin na Amirka suka nuna hoton vidiyon 'yan sanda suna kokarin shiga hidan mutumin.

XS
SM
MD
LG