Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama Tsakanin 'Yan Banga Da Mutanen Gari A Kontagora Ya Halaka Mutane 4.


Hoton wani jami'in 'Yansanda a Najeriya.

Ana zargin 'yan banga sun kashe wani matashi kan wani zargi da zuwa yanzu ba'a bayyana ba.

A jahar Nija, an kashe akalla mutane hudu a yankin kontagora, a wata arangama tsakanin mutanen gari da ‘yan banga.

Wani da aka yi lamarin kan idonsa mai suna Mohammed Nura Usman, ya gayawa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa, wasu ‘yan banga ne suka kama wani matashi bayan da aka tashi daga kallon kwallo bisa zargin aikata wani laifi da ba’a fayyace ba. Suka rika yi masa duka har sai da ya mutu.

Bayan da aka dawo da gawarsa, mutanen unguwar suka fusata, suka yi zanga-zanga har zuwa ofishin ‘Yan bangan har suka kona ofishinsu.

A nasu maratnin, inji Nura, ‘yan bangan suka je gidan da matashin nan yake da zama, suka rika jifa suna hayaniya, suka kuma bude wuta kan mazauna gidan suka harbe matasa uku da mace daya.

Kakakin rundunar ‘Yansanda na jahar DSP Bala Elkanah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace zuwa yanzu basu da adadin wadanda rikicin ya halaka. Domin jami’ansu suna ci gaba da aiki a yankin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG