Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Libya Da Dama


Akalla mutane dari da arba'in ne aka kashe a wani hari da aka kai a kasar Libya

A kasar Libya an kashe mutane akalla 141 da aka ce galibinsu duk soja ne dake rundunar LNA dake karkashin jagorancin General Khalifa Haftar, a cikin harin da aka kai akan barikin sojan dake kudancin Libyar a jiya Jumu’a.

Wani kakakin rundunar ta LNA Ahmad al-Mismari ya gayawa kampanin dillacin labaran AFP cewa dakarun dake biyayya ga gwamantin GNA ta Libya mai goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ne suka kai farmaki.

Kakakin yace sojan da aka kashe suna dawowa ne daga wani fareti don haka basa dauke da makamai lokacinda aka abka musu, kuma aksarinsu kisan gilla aka yi musu na nan take.

Sauran wadanda suka rasa rayukkansu duk fararen hula ne dake aiki a barikin da kuma wadanda kaddara ta rutsa da su a wurin.

Sai dai tuni jami;an gwamnatin ta Libya suka la’anaci farmakin kuma suka musanta cewa suna da hannu a cikinsa. Haka kuma gwamantin tace zata dakatarda ministan tsaro al-Mahdi al-Barghati daga aiki har sai an gano gaskiyar abinda ya faru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG