Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

An Kashe Wata Mai Fafutukar Kare 'Yancin Mata

Sabeen Mahmud

An kashe wata mai fafutukar kare 'yancin mata a Pakistan yau din nan bayan ta fito daga wani taron da suka shirya a yankin Baluchistan.

Firaministan Pakistan Nawaz Shariff yayi Allah wadai da harin da aka kai tare da bada umarnin yin binciken kashe fitacciyar ‘yar rajin kare hakkin mata Sabeen Mahmud a birnin Karachi. Haka ma ofishin jakadancin Amurka da ke Islamabad ma yayi tir da wannan kisan na Sabeen sannan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da abokan marigayiyar.

Wasu ‘yan bindiga ne akan Babura suka kasheta jim kadan bayan ta fito daga wani taron da ta shirya a shagonta da aka fi sani da T2F ita da mahaifiyarta Mehnaz Mahmud a kudu maso gabashin yankin Baluchistan kamar yadda ‘yan sanda suka fada. Yankin Baluchistan dai yayi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci bat un yau ba.

Firaministan Pakistan Nawaz Shariff yayi Allah wadai da harin da aka kai tare da bada umarnin yin binciken kashe fitacciyar ‘yar rajin kare hakkin mata Sabeen Mahmud a birnin Karachi. Haka ma ofishin jakadancin Amurka da ke Islamabad ma yayi tir da wannan kisan na Sabeen sannan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da abokan marigayiyar.

Masu bincike dai basu ce komai ba amma yan uwa da abokan Sabeen sunce wannan kisa ne da dama ita aka yi niyyar kashewa. Bayan an harbeta an yi kokarin zuwa asibiti amma ta cika a hanya. Likitoci sun tabbatar da cire harsasan bingiga guda 5 a jikinta. Itama mahaifiyarta na nan tana jinyar harbin da aka mata a lokacin.

Da sanyin safiyar yau ne dai Sabeen ta shirya taron a shagonta game da danne hakki a Baluchistan tare da gayyato AbdulQadeer Baluch da Farzana Baluch a matsayin baki masu jawabi. AbdulQadeer dai ya fadawa jaridar Pakistan cewa,

“Ba wanda bai san su wa suka kashe Sabeen ba” amma bai yi wani Karin bayani ba. Kirarin ta dai a yanar gizon T2F shine, “Wacce Aka Haifa Da Azamar Kawo Canji Ga ‘Yan Birinin Pakistan”.

XS
SM
MD
LG