Accessibility links

'Yan Bindiga A Kenya Sun Kashe 'Yan Sanda 34 A Arewacin Kasar.


Jami'an 'Yan Sandan Kenya suke sintiri a harabar wani coci bayan wani hari da aka kai.
‘Yan bindiga a arewacin Kenya sun kashe ‘yan sanda akalla 34 wadanda ke farautar barayin shanu, a wani lamarin da aka bayyana a zaman daya daga cikin hare-hare mafiya muni da aka taba kaiwa kan ‘yan sanda a tarihin kasar.

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta ce an yi kwanton bauna aka far ma ‘yan sandan a lokacin da motarsu ta shiga cikin wata gunduma mai suna Baragoi dake cikin lungu sosai a arewacin kasar. Jami’ai suka ce mutane tara sun kubuta kuma su na jinya a asibiti. Suka ce har yanzu akwai wadanda ba a san inda suke ba.

Kakakin ‘yan sandan Kenya, Eric Kiraithe ya lashi takobin cewa za a kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Har ila yau yace ‘yan sanda su na sake nazarin tsarinsu na fita aiki a yankin domin tabbatar da cewa irin hakan bai sake faruwa ba.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin, amma ‘yan sanda su na kyautata zaton cewa barayin shanu su ne suka kai wani hari makamancin wannan a watan da ya shige a gundumar ta Baragoi har suka kashe mutane 13.
XS
SM
MD
LG