Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe yara 'yan makarantar firamari a Maiduguri


(File Photo)

'Yan bindiga sun kashe yara kanana 'yan firamari a harabar makarantarsu yayin da suke rubuta jarabawa wai domin su da iyayensu suke nuna 'yan Boko Haram ga jam'an tsaro

Wasu 'yan bindiga sun shiga harabar wata makarantar firamari a birnin Maidugurin Najeriya inda suka bude ma yara kanana wuta. Sun kashe wasu da dama cikin yaran.

Wannan harin a kan yaran da basu ci basu sha ba tamkar maida martani ne a kan iyayen yaran inji su maharban. Sun zargi yaran da iyayensu da cewa su ne suke tseguntawa jami'an tsaro inda su 'yan Boko Haram suke.

Idan dai ba'a manta ba kwana kwanan nan matasan Jihar Borno musamman a Maiduguri suka shiga farautar 'yan kungiyar Boko Harma suna kamasu suna mikawa jami'an tsaro. Har ma domin cimma nasara da zata yi tasiri sun bukaci gwamnati ta taimakesu da kayan yaki.

Abokiyar aiki a Muryar Amurka Jummai ta samu ta zanta da wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum inda ya roki 'yan Boko Haram da su yi hakuri su manta da abubuwan da suka faru a baya can tun da an soma shirin sulhuntawa. Ya kira su da su kai zuciyarsu nesa domin a samu zaman lafiya.

Ga karin bayani a wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG