Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kira Majalisar Dinkin Duniya Ta Gudanar da Bincike Akan Kashe kashen Mutane a Kwango Kinshasha


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Antonio Guterres

Hukumar kare hakin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kira a gudanar da binciken kasa da kasa bisa kashe kashen mutane a Kwango Kinshasha da tace sau tari ma sojojin kasar ke bada umurnin kashe mutanen.

Shugaban hukumar kare hakiin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, yayi kiran da a gudanar da bincike na kasa da kasa kan kashE kashen da aka yi a yankin tsakiyar Kwango Kinshasa, ya kuma dora wani bangaren laifin wannan kan gwamnatin kasar wadda ta kasa dakatar da kashE kashen.

Zeid Ra’ad al-Hussein ya fadawa majalisar kare hakkin bil Adama yau Talata cewa a cikin watanni biyun da suka shige, an kashE daruruwan mazauna kauyuka ta hanyar harbewa, ko sassarewa ko kuma konawa kurmus.

Zeid yace a wasu lokutan, jami’ai daga rundunar soja da ta ‘yan sanda suka rika bayarda umurnin aikata kashe kashen.

A cikin wannan makon ake sa ran hukumar kare hakkin bil adama ta MDD zata jefa kuri’a kan wani kuduri na kafa hukumar bincike mai zaman kanta game da wannan tashin hankali a yankin Kasai na Kwango, ciki har da kashe wasu kwararru na MDD su biyu da aka yi cikin wannan shekara.

Ministan shari’a na Kwango, Alexis Thambwe Mwamba, yayi watsi da kiran gudanar da binckke na kasa da kasa, yana mai cewa ba zai yiwu a kaddamar da irin wannan bincike ba, ba tare da sanya jami’an gwamnatin Kwango a ciki ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG