Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Peter Strzok Daga Cikin Kwamitin Da Robert Mueller Ke Shugabanta


Jamian hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a yayin wani aikin bincike a massachusset

An kori daya daga cikin masu aikin binciken kwamitin da Robert Mueller kewa jagoranci game da alakar tsohon mai baiwa shugaba Trump shawara a harkokin tsaro da Rasha.

Sananne kuma fitaccen wakilin a FBI, wanda kuma lauya ne dake cikin kwamitin binciken nan da Robert Mueller ke aikin bincike na musammam game da kutsen da ake tuhumar Rasha tayi a zaben Amurka na shekarar 2016 yanzu an fidda shi daga cikin wannan kwamitin da Mueller yake wa shugabanci

An dai sallami Peter Strzok ne a kusan karshen watan yuli bayan shi da wata mata dake cikin kwamitin binciken sun gano cewa lauyan na hukumar ta FBI sunyi musayar wasu bayanan dake shafin Email din wadanda basu goyon bayan Trump da masu goyon bayan Hillary.

Mai Magana da yawun Mueller yace an cire wannan wakilin na FBI ne sailin da aka ji wannan zargin, yanzu haka dai shi wannan lauyan ya bar wannan kwamitin sailin da wannan batu ya fito sarari.

Da ffarko dai an danka wa shi Strzok aikin binciken anfani da runbun tattara bayanai adireshin email mallakar Hillary ne data yi anfani dashi lokacin tana sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG