Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kubutar Da Mutum Kusan 100 A Arewacin Najeriya

An Kubutar Da Mutum Kusan 100 A Arewacin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:26 0:00

An kubutar da kusan mutum 100 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da mata da yara kanana, sama da wata biyu bayan da ‘yan bindiga suka sace su a arewa maso yammacin Najeriyar a cewar ‘yan sandan kasar.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Zamfara, Ayuba Elkana, ya ce daga cikin mutum 97 da aka kubutar 19 jarirai ne da kuma yara kanana da dama.

Yayin da ake sauke su a motocin bas ba takalma a kafafunsu a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara, an ga mutanen cikin yanayi na gajiya sanye da tufafin da suka tsufa.
XS
SM
MD
LG