Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Kan Iyakokin Najeriya Da Kamaru


Sojojin Najeriya

An rufe kan iyakokin Najeriya da kamaru bisa yarjejeniya tsakanin kasashen da nufi kakkabe mayaka masu kaifin kishin Islama

Sojoji da suka karbi ragamar tsaron a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da aka ayyana dokar-ta-baci sun rufe kan iyakokin Najeriya da kasar Kamaru da nufin shawo kan mayakan da suka addabi jihohin bisa ga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu.

Jami’an gwamnatin jihar Adamawa da suka hada da majalisar dokokin jihar sun yi kira ga al’umma su bada hadin kai su kuma kasance masu kiyaye doka da oda domin ganin an sami zaman lafiya cikin sauri abinda ake bukata kafin janye dokar ta bacin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG