Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saba Ma Yarjajjeniyar Zaman Lafiyar Sudan Ta Kudu


Shugaban Sudan Omar al-Bashir ke daga hannun Kiir da Machar bayan cimma yarjajjeniyar da yanzu aka saba ma wa.
Shugaban Sudan Omar al-Bashir ke daga hannun Kiir da Machar bayan cimma yarjajjeniyar da yanzu aka saba ma wa.

Da alamar dai ta leko ta koma ga yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin Shugaba Salva Kiir na Sudan Ta Kudu da 'yan tawaye.

'Yan sa'o'i kawai bayan da yarjajjeniyar zaman lafiyar da Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da 'yan tawaye su ka cimma ta fara aiki an saba ma ta; kuma kowane bangare na zargin dayan da fara kai hari a wannan kasar ta yankin tsakiyar gabashin Afirka.

Mai magana da yawun 'yan tawaye Lam Paul Gabriel ya zargi sojojin gwamnati da kai hari kan dakarun 'yan tawaye a bayan birnin Wau, bayan sa'o'i shida kawai da yarjajjeniyar ta fara aiki.

Shi kuma mai magana da yawun gwamnati Ateny Wek Ateny, ya gaya ma kamfanin dillamcin labarai na Associated Press cewa 'yan tawayen ne su ka fara kai hari har su ka nemi uzuhuri bisa hujjar cewa, "Ba su da kintsattsan jagoranci. Ba su kuma da takamaiman shugaba."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG