Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto


Aminu Bagaji Bodai, Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto
Aminu Bagaji Bodai, Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto

An sace Aminu Magaji dan majalisar mai wakiltar Karamar Hukumar Dange Shuni ne i a daren jiya a gidanshi dake kauyen Bondi mai tazarar kilomita goma sha biyar daga babban birnin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa yan Bindigar da aka kiyasta adadinsu su 10, sun shiga garin na Bodai dake karamar hukumar mulki ta Dange Shuni mai tazarar km 20 da babban birnin jiha, da misalin karfe 1 na daren jiya, inda kuma suka zarce kai tsaye zuwa Gidan dan majalisar dokokin Aminu Magaji Bodai, suka kuma yi awon gaba da shi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bakin kakakinta SP Muhammad Abubakar.

Manazarta lamurran tsaro dai na ganin wannan manuniya ce na yadda kalu balen tsaro da ya fi shafuwar talaka a da, ke kara uzzura a jihar ta sokoto.

Wannan ko yana zuwa ne mako daya bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka sace wata Mata mai juna biyu hade da yarta, a kauyen katsira dake karamar hukumar mulkin ta Dange Shuni, wacce rahotanni suka ce an sako ta da safiyar yau, bayan da aka ce an biya naira miliyan daya a matsayin kudin fansa.

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna

An sace dan majalisar dokokin jihar Sokoto-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG