Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Mahaifiyar Mataimakin Gwamnan JIhar Taraba


'Yan Sandan Najeriya.

Rahotanni daga jihar Taraba Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun sace mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Taraba, Hon. Haruna Manu.

Yanzu haka dai ba’a san inda aka yi da mahaifiyar mataimakin gwamnan ba, lamarin da yasa jama’a cikin yanayin alhini da fargaba.

Kamar yadda wasu ‘yan garin suka bayyana sunce wasune da ba a san ko su waye ba dauke da bindigogi sukayi shigar burtu a garin, har sukayi awon gaba da mahaifiyar mataimakin gwamnan, wanda har ya zuwa yanzu babu wanda yasan inda akayi da ita.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro a jihar ba suyi karin haske ba, domin ko da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Joseph Kwaji, yace bashi da cikakken bayani a yanzu. Amma yayi kira ga jama’a da su taimaka bayanai domin samun hanyar ceto mutanen da aka sace.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG