Accessibility links

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ministan man fetur na Nigeria Dr. Shettima Ali Munguno jim kadan bayanda aka gama sallar jumu’a a Maiduguri.

Yau ne wasu matasa dauke da makamai suka yi awon gaba da tsohon ministan man fetur na Nigeria, Dr. Shettima Ali Munguno jim kadan bayanda aka kamalla sallar jumu’a a daya daga cikin masallatan birnin Maiduguri. Ance ‘yan bindiga din sunzo ne akan kekensu mai kafa ukku, aka yi salla tareda su, sannan suka umurci wadanda ke tareda Dr. Munguno a cikin motar da su fice, kana suka tafi da shi. Ibrahim Garba Ka-Almasih ya zanta da wakilinmu na Maiduguri, Haruna Dauda kan abinda ya faru:

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG