Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Wata Baturyar Mishan Ba'amurkiya a Kogi


Rev.Phyllis Sortor Wadda aka sace jiya Litini
Rev.Phyllis Sortor Wadda aka sace jiya Litini

Wata Ba'amurkiya mai aikin Mishan ta fada hannun masu satar mutane don neman kudin fansa, a Jihar Kogi dake Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga da fuskoki rufe sun sace wata ba amurkiya mai aikin Bisharar Mishan ‘yar shekra 65-70 da haihuwa a yankin tsakiyar Najeria, kuma ana kyautata zaton an kamata ne don neman kudin fansa a cewar ‘yan sanda a yau din nan.

Kafar yada labarai ta AFP ta ruwaito mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kogi Sola Collins Adebayo na cewa , “an sace ta ne litini da misalign karfe 10:00 na safe agogon yankin.

Yace al’amarin ya auku ne a kauyen Emiworo,inda turawan Mishan na Majami’ar Free Baptist ke tafi da wata kungiyar muradun al’umma a harabar wata makaranta mai alaka da Majami’ar.

Wani bayani a dandalin internet na Majami’ar na nauke da sanarwa makamanciyar haka, inda aka ruwaito Bishop David Kendal na cewa tuni ma aka sanar da Ofishin Jakadancin Amurka da kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG