Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sake kashe mutane 15 a jihar Plato


An kashe akalla mutane goma sha biyar , bayan wani hari da aka kai cikin dare a kauyen Wvang Kobot kusa da birnin Jos jihar Plato a arewacin Nigeria inda aka kashe mutane da dama tun watan Augusta a sakamakon rikicin kabililanci data addini.

An kashe akalla mutane goma sha biyar , bayan wani hari da aka kai cikin daren juma'a a kauyen Wvang Kobot kusa da birnin Jos jihar Plato a arewacin Nigeria inda aka kashe mutane da dama tun watan Augusta a sakamakon rikicin kabilanci data addini.

Jiya asabar mai magana da yawun gwamnatin jihar Plato Mr Ayuba Pam ya fadawa wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji cewa mutane goma sha biyar ne aka kashe. Yace gwamnatin jihar Plato tayi wani taro akan wannan hari, da kuma tattauna matakan da zata dauka domin tabbatar da am samu zaman lafiya jihar Plato.

An dai kai wannan hari ne kwana daya bayan da jami’ai suka ce an kashe wani mutum da yayansa bakwai anan jihar Plato din. Kumai tama Majalisar Dikin Duniya a ranar juma’a ta baiyana damuwa akan tarzomar data ce sun kashe kimamin mutane saba’in tun watan Augustan

XS
SM
MD
LG