Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yin kira ga Gwamnatin Tarayya ta Ceto Wadanda Boko Hara Ta Sace


Mr. Solomon Yusuf wanda Boko Haram ta sace dansa yayi gangami da BBOG Kungiyar dake fafutikan ganin an sako sauran 'yan matan Chibok tayi maci a Abuja
Mr. Solomon Yusuf wanda Boko Haram ta sace dansa yayi gangami da BBOG Kungiyar dake fafutikan ganin an sako sauran 'yan matan Chibok tayi maci a Abuja

Cikin wadanda suka gudanar da zanga zangar lumana da kungiyar BBOG ta kaddamar makon jiya a ci gaba da fafutikar ganin an sako sauran ‘yan matan Chibok, akwai wadanda aka sace ‘yan uwansu kwanakin baya.

Wadanda suka shiga zanga zangar lumana da kungiyar BBOG tayi suna kira ga gwamnati data taimaka a sako malaman jami’ar Maiduguri, jami’an da suke neman man fetur, da matan ‘yan sanda da dai sauransu da ‘yan Boko Haram suka sace.

Nehemiah Yusuf mahaifin Mr. Solomon Yusuf, malami a jami’ar Maiduguri da aka sace yace tun daga lokacin da aka sace dansa da abokan aikinsa a watan Yuli basu ji komi ba. Dalili ke nan da ya sa suka fito domin su nunwa gwamnati damuwarsu.

Ita ma Esther Manzo ‘yar uwarta aka sace a garin Damboa a jihar Borno. Tace a watan Yunin da ya gabata zasu kai gawar wata ‘yar uwarsu ne suka ci karo da ‘yan Boko Haram nan take suka sacesu.

Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG