Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Tsohon Shugaban Kasar Misra Husni Mubarak Daga Gidan Yari


Tsohon Shugaban Kasar Misra Husni Mubarak
Tsohon Shugaban Kasar Misra Husni Mubarak

An saki Tsohon shugaban kasar Misra Hosni Mubarak bayan kwashe shekaru shida da yayi a tsare a gidan yari da kuma Asibiti, biyo bayan  Juyin juya halin da akai a kasashen larabawa a shekarar 2011.

Tsohon shugaban ya bar Asibiti a yau Jumu’a. Mubarak dai shine shugaban Misra na farko da ya fuskanci shari’a bayan juyin juya halin na kasashen larabawa da mamaye yankin.

An tuhume shi da tada husumar da tayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da suka rasa rayukkansu a lokacin wannan zanga zangar da aka share kwanaki 18 ana gudanarwa.

Sannan an tuhumeshi da wasu laifuffukan da daga baya aka watsar dasu. Lauyan Mubarak ya tabbatar da tsohon shugaban yanzu yana zaune cikin lumana a gida a wata unguwa ta masu hannu da shuni mai suna Heliopolis.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG