Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Dino Melaye Bayan Cafkeshi


Sanata Dino Melaye

An sako Sanata mai wakiltar mazabar yankin Kogi ta yamma bayan da aka tsareshi yau a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, mai magana da yawun sanatan Gideon Ayodele, ya shaidawa manema labarai cewa, an sako Sanatan bayan sa'o'i biyu da tsareshi.

"'Yan Sanda sun sakeshi bayan sun gaza gano laifi akansa," inji Ayodele

A yau ne Sanata Dino Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, an tsareshi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe yayin da yake kokarin tafiya kasar Morocco domin aiki.

A baya dai 'Yan Sanda na zargin Melaye da kin bayyana a gaban kotu don fuskantar shari'a, a bisa zargin da ake masa na daukar nauyin wasu bata-gari da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG