Accessibility links

An Sallami Hillary Clinton Daga Asibiti


Sakatariyar Ma'aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tana barin asibiti tare da mijinta, Bill (TOP R), da yarta Chelsea
An salami sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a asibitin dake birnin NY inda aka kwantar da ita na tsawon kwanaki sabili da samun gudajin jinni da aka yi a cikin kanta.

Clinton ta bar asibitin Presbyterian dake NY jiya Laraba da yamma tare da maigidanta tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton da kuma ‘yarta Chelsea.
Wata sanarwa da aka bayar a hukumace tace tawagar likitocin dake kula da sakatariyar sun ce tana samun sauki yadda ya kamata, suka kuma hakikanta cewa zata murmure baki daya.

Tun farko da rana, ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace, Clinton tana magana da ma’aikatan ofishinta a Washington ta wayar tarho wadanda suke kula da harkokin kasashen ketare yayinda take jinya. Sanarwar bata bayyana lokacin da zata koma bakin aiki a Washington ba.

An kwantar da Clinton a asibiti ne ranar Lahadi sabili da samun gudajin jini cikin jijiyarta bayan sumar da tayi a tsakiya watan Disamba. Clinton ta fadi ta buge kai lokacin da take jinya a gida na ciwon ciki da take fama da shi. Babbar jami’ar diplomasiyar ‘yar shekaru 65 bata bayyana a bainin jama’a ba tun farkon watan da ya gabata.
XS
SM
MD
LG