Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami kananan yara 72 da kwayar cutar Polio bana a Najeriya


Ma'aikatan sa kai suna rigakafin shan inna
An sake samun kananan yara biyu dauke da kwayar cutar shan inna a Najeriya, abinda ya kai adadin yaran da aka samu da cutar zuwa 72 bana.

Rahoton da shirin yaki da cutar shan inna na duniya da ake kira da turanci “Global Polio Eradication Initiative “ ko kuma GPEI a takaice, ya bayar na nuni da cewa, an sami kananan yaran dake dauke da kwayar cutar ne a jihar Kasina.

Shirin yaki da cutar shan inna ya kuma sanar da dage shirin rigakari da kari da ya kamata a gudanar farkon watan Satumba zuwa karshen watan sabili da dalilan tsaro, wanda bisa ga cewar shirin yana daya daga cikin kalubalai da ake fuskanta a yunkurin shawo kan cutar.

Ana kuma shirin gudanar da aikin rigakafi a mazabu hudu na jihar Taraba inda aka sami bullar kwayar cutar a cikin watan jiya, yayinda kuma ake kyautata zaton fadada aikin rigakafi a yankin hamhuriyar Nijar dake kan iyaka da jihar Katsina, ganin yadda a bana aka sami kananan yara 14 dauke da kwayar cutar a jihar.

Shirin GPEI, shiri ne da ya hada kan masu ruwa da tsaki a harkokin kiwon lafiya da ya hada da asusun tallafawa kananan yara na duniya UNICEF, da Hukumar lafiya ta Duniya WHO, da kulob din Rotary da kuma cibiyar yaki da cututuka ta Amurka CDC, wadanda ke da manufa daya, ta shawo kan cutar shan inna a kasashen duniya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG