Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami sabbin kashe-kashe a sashin bakin tekun Mexico


Jami'an tsaron Mexico kenan ke aikin tabbatar da tsaro

Sojojin Ruwan Mexico sun ce an gano gawarwakin mutane 32 a jihar

Sojojin Ruwan Mexico sun ce an gano gawarwakin mutane 32 a jihar Veracruz da ke gabashin kasar, inda aka watsar da wasu dinbin gawarwaki kan hanya da tsakar rana a watan da ya gabata.

An gano gawarwakin ne jiya Alhamis cikin wasu gidaje 3 da ke wata tashar jirgin ruwa, wadda ta zama tamkar fagen munanan fadace-fadace tsakanin masu safarar muggan kwayoyi.

Hukumomi na kyautata zaton masifaffiyar kungiyar “Zetas” ta masu safarar muggan kwayoyin nan na da hannu a mutuwar mutane 35 da aka gano gawarwakinsu a watan jiya an watsar bisa wata babbar hanyar cikin gari a Veracruz.

Shugaba Felipe Calderon ya girke ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a Veracruz.

An hallaka sama da 40,000 a Mexico tun bayan da Shugaba Calderon ya kaddamar da shirin yaki da safarar muggan kwayoyi a 2006.

XS
SM
MD
LG