Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Karuwar Masu Dauke Da Zazzabin Lassa a Najeriya


Wata bera

A Najeriya cibiyar kare cututtuka masu yaduwa, wadda ake kira NCDC a takaice, ta bayyana cewa a watanni ukun farko na wannan shekarar, an samu karuwar mutanen da suka kamu da zazzabin Lassa wanda bera ke haddasawa.

A shekarar bara a daidai wannan lokaci ne aka samu bayanin kamuwa da cutar zazzabin Lassa har sau 1801.

Daga ciki, mutum 114 ne suka mutu sanadiyyar zazzabin a jihohi 21, a yayin da a wannan shekarar, a watanni ukun farko, alkaluma na nuni da cewar an samu rahoton kamuwa da zazzabin Lassa har sau 3735.

Wasu mata da ke jinyar ‘yar uwarsu wacce ke dauke da cutar sun shaida wa Muryar Amurka cewa ana nuna musu kyama da tsangwama.

“Ba a dauki masu cutar da wani muhimmanci ba, maimakon a taimaka musu yadda ya kamata amma sai ka ga gudunsu ma ake yi,” a cewarta.

Daga cikin mutane 3735 da aka samu labarin cewa suna dauke da cutar, an tabbatar da guda 906, a yayin da mutane 161 su ka mutu a sanadiyar zazzabin a jihohi 27.

Facebook Forum

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG