Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Nakiyoyi Masu Dimbin Yawa cikin Wani Gida a Jihar Connecticut ta Amurka


Gwamnan Jihar Connecticut Dannel Malloy

An sami nakiyoyi masu dunbin yawa a wani gida dake garin New Haven Jihar Connecticut dake Arewa maso gabashin Amurka.

Jami’an ‘Yan sanda sunce basu san yadda mamallakin wadannan nakiyoyi yayi niyyar amfani da su ba musanman ta ganin yadda aka sami nakiyoyin a cikin kusan kowanne daki a gidan.

An kira ‘Yan sanda gidan ne sakamakon wata ‘Yar hayaniya ta cikin gidan.

An tuhumi Pasquale Criscio ranar Alhamis da laifin mallaka da kuma ajiye makamashi tare da hada nakiyoyi ba kan ka’ida ba. Mallakar Nakiyoyin da aka haramnta da kuma laifuka guda biyu na saka kananan yara cikin hadari. A lokacin da ‘Yan sanda suka isa gidan sun tarar da yara kanana da suka hada da Mai kimanin shekaru 15 da kuma Shekara 6 a cikin gidan.

Jami’an ‘Yan sandan sun kara da cewa sinadaran da aka samu a gidan sunyi kama da irin wadanda aka yi amfani dasu a harin da aka kai yayin tseren famfaleke Boston a wata shekara inda wasu wa da kani suka shirya bamabamai.

Babban jami’in Yan sanda John Alston ya fadawa jaridar New Haven Register cewa yawan nakiyoyin da aka samu da sinadaran da ke cikin gida da bakar hodar harsashi “ da wani abu ya faru to da gaba dayan Unguwar da duk wadanda suke ciki da lokaci ya kure musu.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG